Technology

Yadda Zaka Sake Fito Da Slip Na National Id Card Idan Ya Tsufa Ko Ya Goge

Matsalar gogewar rubutun dake kan National ID Card kokuma  Tsufansa matsalace da ake samunta dayawa a sassan kasarnar a sakamakon rashin fitowar original ID card.

To amma ta yaya zan iya dawo dashi idan nafada daya daga cikin matsalolin da muka ambata a sama?

Hanyar da ake bi domin sake printing na National ID Card din itace muka takaita muku ita kamar haka:

Zaka danna wannan LINK.

Sai ka zabi NIN SLIP REISSUE sannan kacigaba da cike sauran bayanai, akarshe zaka biya N500 dakuma sauran cajin da  remitake caja.

Bayan ka kammala ka tabbata kayi download ka kuma yi printing na shaidar biyan kudin da kayi,domin da wannan sheda ne za’a gane ka biya.

Sannan kuma zaka tafi office din NIMC (National Identity Management Commission) da takardar Affidavit na Sake printing Slip da kuma Tsohon naka National ID Slip.

Shikenan sai suyima printing Sabon Slip na National ID Card.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button