Education

Yadda Ake Duba Result Na Science and Technical Schools Board, Kano State

A sakamakon cigaban da aka samu a yanzu za’a iya dubawa dalibai sakamakon jarrabawar ta hanyar amfani da wayar hannu kana daga gida.

Hanyoyin da akebi domin duba sakamakon sune kamar haka:

Step 1: Abu na farko shine za’a shiga shafin makarantar na yanar gizo-gizo ta wannan adireshi www.stsbkano.ng.

Step 2: Abu na biyu shine bayan shafin ya bude daga tsakiyarsa za’a ga ansa Apply da Login sai a danna Login.

Step 3: Abu na uku shine bayan an danna Login zai baka damar kasaka User Name da kuma Password, User Name din da ake amfani dashi ita Examination Number wacca tafara da Alphabet masu manyan baki wanda yake akan takardar da akayi rijista, shikuma Password shine shekarun haihuwa na dalibin wadanda akayi amfani dasu a lokacin rijistar, kuma a sanya su a yadda sukazo.

Step 4: Abu na hudu shine bayan an shigar da User Name da kuma Password sai a danna Login daga nan bayanan dalibi zai fito daga kasa a gefen hannun hagu za’a ga inda akasa Print Exam Result sai a danna shi sakamakon zai bude, daga karshe sai ayi printing ko ayi save dinsa akan wayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button