Education

Gwamnatin Jihar Kano ta Bawa Dalibai Hutun Makaranta Domin Suyi Murmushi

Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano bisa sahalewar Gwamnatin jihar Kano ta amince da hutun kwana 5 ga dalibai.

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta amince da hutun kwanaki 5 ga dukkan Makarantun Firamare dana gaba da firamare dake aiki a jihar Kano

hutun zai fara aiki ne daga Talata 11 zuwa Litinin 17 ga Mayu 2021.

A cewar sanarwar, Shugabannin Malamai da Shugabanni za su tabbatar da cewa duk daliban makarantar kwana za su koma makarantunsu a ranar Lahadi 16 ga wata yayin da makarantun Jeka kadawo za su koma makarantunsu a ranar Litinin 17 ga Mayu 2021.

Sanarwar ta kuma yi gargadin cewa duk daliban da abin ya shafa dole ne su koma makarantunsu a ranakun da aka kayyade, domin matakin ladabtarwa da ya dace na jiran wadanda suka gaza komawa.

A karshe muna kirah ga iyayen yara da Suyi kokarin bin umarnin Gwamnati wajen daukar yaransu lokacin da akai hutu dakuma mayar dasu ranar da aka bada umarnin komawa domun cigaba da karatunsu Kamar yadda aka saba.

Allah yataimaki Mai girma Gwamnan jihar kano da dukkanin masu taimaka masa akan harkokin ilimi.

Hon jilani Al-Mustapha danmalam
Babban Maitaimakawa mai girma Gwamna akan Ilimi
7-5-2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button