Education

YADDA AKE SAMUN ADMISSION TA HANYAR JAMB UPLOADING RESULT

YADDA AKE SAMUN ADMISSION TA HANYAR JAMB UPLOADING RESULT

Dayawan dalibai na rasa admission a dalilin rashin dora sakamakon jarrabawarsu  kodai na WAEC ko NECO a Jamb Portal bayan fitowar jamb resul a kowace shekara.

Da zarar ance sakamakon jarrabawa ya fito, a dai dai wannan lokaci ne duk wanda yasan bai dora result dinsa na SSCE a cikin Dashboard dinsa na Jamb to lallai ya hanzarta yaje kowane CBT Center dake a fadin kasarnan domin a dora masa, rashin yin haka kansa ya rasa admission kodai na jami’a ko na College a duka makarantun kasa.

Kamar yadda aka bayyana a sama cewar dawan dalibai na samun admission daga jami’a amma a sakamakon rashin wannan result uploading kan sanya hukumar jamb ta hana dalibi admission wanda hakan kansa dalibi ya rasa admission wanda jami’ar daya nema ta bashi.

Bayan haka, yanada kyau dalibai su sani cewar result kan iya sauka a portal na Jamb a sakamakon dalilai da dama wadanda baza’a iya tantancesu ba. Don haka yanada kyau dalibi ya tabbatar yana duba dashboard dinsa na Jamb domin ganin bashida wata matsala don kaucewa wannan barazana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button