Education

NECO TA SANAR DA RANAR SAKIN SAKAMAKON JARRABAWAR SHEKARAR 2021

Shugaban hukumar jarrabawar NECO (National Examination Council) professor Ibrahim Wushishi ya sanar da cewar dalibai miliyan daya da dubu dari uku ne suka zauna jarrabawar  SSCE (Senior Secondary School Examination) a duka fadin kasar nan a inda yace za’a saki sakamakon a tsahon sati uku kacal.

Shugaban ya sanar da hakanne a lokacin hira da manema labarai a babban birnin Yola dake Adamawa cewar dazarar an kammala jarrabawar hukumar zata fara maka ta domin ganin sun cimma alkawarin da sukayi. Professor Wushishi yace a tsahon sati biyu zuwa uku (3rd September 2021) zasu kammala maka  jarrabawar.

Babban jami’in ya kara da cewar sun shirya tsaf domin fara gwada jarrabawar Objective a sabon jadawalinnan na Examination computer Based a inda hukumar zata kara karkade matsalar nan ta magudin jarrabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button