Education

Kano Scinece and Technical Board Sun Fara Bayar da Admission 2021/2022

Ɗaliban jahar Kano masu yawa ne suka zauna Nemi wannan Makaranta ta Kano Scinece and Technical Board domin cigaba da samun ingantaccen ilimi, bayan gudanar da jarrabawa da makaranta tayi, sakamakon jarrabawar ya fita inda wasu suka haye wasu kuma basu sami gurbin kartu a makarantar ba sakamakon mark ƌinsu bai kai ba.

A halin yanzu kuma makarantar ta Kano Scinece and Technical Board ta fara bayar da Admission na zango karatun shekarar 2021/2021 ga dukkan daliban da suka sami nasarar cinye jarrabawar da suka yi a baya.

Hukumar makarantar ta sanar da hakan ne ta shafinta na yanar gizo-gizo domin sanar da Ɗalibai da iyayen daliban akan lokaci.

Za’a iya duba admission na wannan makaranta ta wayar hannu ko kuma ta hanyar yin amfani da computer ta shafin da hukumar makarantar ta samar.

Za’a iya ziyartar internet café mafi kusa domin samun admission ƌin a sawwaƙe, sannan wajibi ne dukkan dalibin dake son cire admission da yazo da takardar sa wace take dauke da user name da password na ƌalibi domin sai dashi ne za’a iya samun damar cire admission ƌin.

Duba Admission: https://www.stsbkano.ng/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button