Education


School Of Health Technology Kano, School Of Health Technology Bebeji And School Of Hygiene Kano Sales Of Form Will Commence


School Of Health Technology Kano, School Of Health Technology Bebeji And School Of Hygiene Kano Sales Of Form Will Commence

Gamayyar Makarantun Lafiya na Jihar Kano sun sanar da ranar da za’a fara sayar da form din shiga makarantar domin fara kartu na shekarar 2022, makarantun sune kamar haka:

  1. School of Health Technology Kano
  2. School of Health Technology Bebeji
  3. School of Hygiene Kano.

Dukkan dalibai da suke da sha’awar shiga wannan makaranta sai su kasance cikin shiri duba da yadda dubban dalibai ke sha’awar shiga makarantar, sannan hukumar makaratar ta sanar da ranar Asabar 5 ga watan February 2022 ne za’a bude shafin makarantar na internet domin fara sayar da form din.

Hukumar Makarantar ta kara da cewa za’a bude a 12:00am na ranar da aka sa za’a bude domin fara sayar da form din.

Sannan dalibi zai iya sayan form din yana daga gida ta shafin internet da hukamar ta samar kamar haka: https://moh.knstate.healthcare/applicants/login

Idan kuma dalibi bai fahimci yadda zai iya saya ba to sai ya ziyarci internet  café mafi kusa dashi domin saya a saukake.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button