Education

Neco Releases External Neco Result 2021

Hukumar shirya jarrawar Neco (National Examination Council) ta bayyana sakin sakamakon jarrabawar private  Neco ta shekarar 2021 a yau Alhamis.

Shugaban hukumar Neco na kasa professor Dantani Ibrahim Wushishi ne ya sanar da sakin sakamakon a inda ya bayyana cewar jimmalar dalibai kimanin 47,917 ne suka zauna jarrabawar, a inda dalibai 45,821 ne suka zauna jarrabawar English a cikinsu dalubai 36,116 ne suka sami credits.

Shugaban ya kara da cewar dalibai 29,342 ne wadanda suke da Math da English sai kuma dalibai 39,991 ne keda sama da 5 credits a math da English.

An sami akalla korafe korafen magudin jarrabawa guda 4,454 wanda a shekarar 2020 aka sami 6465. Shugaban yace an sami saukin magudin jarrabawa a wannan shekara a inda ya kara bayyana cewar hukumar na kara himma wajan magance matsalar magudin jarrabawa a duka fadin kasa ta hanya kara fito da sabbin fasahohin zamani gameda harkar rijistar jarrabawa.

Shugaban ya kara da cewar sunan suna kara himma wajan kara zuburar da ma’aikatansu da kara basu bita wajan samun horo kan makamar aiki. Ya kuma bayyana cewar hukumar na sane da cinkuoson offices da take fama da shi a wasu daga ofisoshinta dake fadin kasar a inda suke kokarin samar da cikakkun kayan aiki ga ma’aikatan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button