Recruitment

Nigerian Air force Sun Saki Jerin Wadanda zasuyi Attasaye (DSSC30/2021)

Dalibai da suka nemi shiga aikin Nigeria Air force zasu shiga atasaye kamar yadda hukumar ta sanar a wata takarda mai dauke da dukkan yadda daliban zasu domin cika ka’idojin da aka gindayawa daliban.

Hukumar tace duba da interview da aka gudanar daga 3-January 2022, to duk wanda yaga sunansa lallai yazama daya daga cikin wadanda zasu hallara a Adreshi kamar haka: NDA Ribadu Campus (Old site) dake Kaduna state a ranar Asabar 5 march, 2022.

Zuwa akan lokaci nada matukar mahimmanci sannan rashin zuwa akan lokacin ka iya haifar da matsala ga candidate.

Abubuwan da za’a taho dasu sune kamar haka:

First leaving certificate

Waec/Neco/ Nabteb Result

HND/Degree Certificate

Birth Certificate/Declaration of age

Letter of state of Origin

Nigerian Air Force Applicant Acknoledgement card

Sign attestation of Parent/guardian consent form and Local Government area attestation form.

Bugu da kari hukumar tace dukkan wadannan takardu za’a zo da photocopy da kuma origina sannan duk wanda baizo dasu ba kada ya zargi hukumar.

Domin Karin bayani sai ashiga wannan adreshi na www.nafrecruitment.airforce.mil.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button