Networking

Yadda Zakayi Linking Layinka da NIN Cikin Gaggawa

Kasancewa an baiwa kowa dama a kasarsa nan day a hada layin wayarsa da NIN dinsa musamman saboda kara tsaro da kuma kara kare hakkin ‘yan kasa.

Tun a baya dai yan Nigeria da dama sun shiga cikin yanayi na rashin jin dadi a lokacin da suka sami labarin cewa za’a datse layukan wayar na duk wanda baiyi linking ba, an bayar da wa’adi akalla sau kusan biyu amma duk da haka wasu basu riga sunyi ba.

Saidai a wannan satin wasu daga cikin ‘yan Nigeria sun fara samun datsewar layin saboda rashin hada layin nasu da NIN number.

Domin hada naka layin wayar na MTN, AIRTEL, 9MOBILE da GLO cikin sauki sai ab wannan hanya.

MTN: *785#

Zaka danna wannan code dake sama da layin naka da kake so kayi linking misalil; 

*785# 1234567890# sai ka tura za’ayi linking nan take, ko kuma ayi amfani da wannan shafin na yanar gizo-gizo  https://mtnonline.com/nin/

GLO:

Shikuma wannan Kamfani na GLO nasa salon linking  din ya sha ban-ban inda shikuma za’a shiga wajen tura sako sai abi wannan ka’ida domin samun Fa’ida; “UPDATE NIN NIN FirstName and LastName” to 109.

AIRTEL:

Sukuwa AIRTEL sun bayar da hanyar cikin sauki domin kuwa babu wata kwana-kwana, da kadauki wayanka zaka danna wannan code *121*1# sai karasa cika bayanai sai ka tura.

9MOBILE:

Suma 9MOBILE wannan code *200*8# suka bayar domin sharewa customers nasu hawaye inda shima za’a danna da layin sai abi ka’idoji domin cikewa, sannan suka kara da hanyar yanar gizo-gizo kamar haka http://www.9mobile.com.ng/nin

Yadda zaka gano NIN dinka idan ta bata cikin sauki sai kayi amfani da wannan code inda zaka gansu sun fito akan wayarka *346#.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button