Technology

Yadda Ake Amfani da eNaira App da kuma abubuwan daya kunsa.

Kamar yadda babban bankin kasa Central Bank Of Nigeria, CBN ya kaddamar da sabon jadawalin kudi wanda akayiwa taken eNaira wanda babban bankin yake cewar shine official Digital Currency na kasa dazai bawa mutane damar hada hadar cinikayya da sauran kudade wato crypto currency.

Babban bankin ya kaddamar da wannan sabon hanyar hada hadar kudi na eNaira a ranar Litinin 25th October 2021 wanda hakan zai bawa duk wanda keda sha’awar amfani da wannan kudi damar fara hada hada dashi ta hanyar da bankin ya samar kamar haka:

  1. Download eNaira merchant wallet a Google play store
  2. Bayan ka sauke sai ka zabi bankinka
  3. Sai kayi creating account ta hanyar abubuwa kamar haka:

i. Email

ii. Phone number

iii. Bank account number

iv. BVN taka

v. RC number (lambar rijistar ka ta kamfani)

vi. TIN number (lambar da akekarba a FIRS)

vii. Business name (wanda kayi rijista a CAC)

viii. Business trading name (wanda kake gabatar da business dashi)

ix. Business category (wane bangare kake business dinka)

4. Sai ka saka password

5. Sai ka kara karantawa ka tabbatar komi dai dai

6. Sai kayi accepting na terms & condition na eNaira policy

7. Sai ka kammala rijistar

8. Sannan ka tuntubi bankinka domin su tabbatar da application dinka

9. Sai kayi activating eNaira merchant wallet dinka

Wadannan sune sharuda da ka’idoji wanda CBN ta kafa domin masu bukatar fara amfani da sabon jadawalin kudi na eNaira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button