Education

Kano State College Of Nursing and Midwifery Ta Sanya Ranar Fara Computer Based Test 2021/2022

Hukumar makarantar Kano State College of Nursing and Midwifery da Kuma Madobi ta sanya ranar fara jarrabawar nan CBT (Computer Based Test) ta daliban da suka nemi makarantar a zangon karatu na shekarar 2021/2022.

 Hukumar makarantar ta sanya ranar Litinin 20th zuwa Ranar Alhamis 23th December 2021 ce raekun da za’a gabatar da wannan jarrabawa ta Computer Based Test. Don haka hukumar makarantar ke sanarwa da duk wanda yasan ya nemi wadannan makarantu daya garzaya zuwa website na makarantar domin cire CBT Identification Slip a ranar Alhamis 16th December 2021 domin sanin inda za’ayi wannan jarrabawa.

Hukumar makarantar ta bada wadannan lambobin waya domin tuntubarta kan Karin bayani ko wata tambaya gameda wannan jarrabawa: 08038889850/08065545101 daga karafe 8:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Yanada kyau duk wadanda suka nemi wadannan makarantu dasu himmanta wajan kokarin cire wannan CBT Identification Slip kafin wadannan raneku. Allah ya bada sa’a min.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button