Education

NIGERIAN DEFENCE ACADEMY KADUNA APPLICATION 2022

Nigerian Defence Academy Kaduna na sanarda dalibai wadanda keda sha’awar shiga wannan makaranta ta horan soja cewar ta bude application na 74th Regular course na shekarar 2021/2022.

An bude wannan application ne ga maza da mata “yan Nigeria  a ranar Litinin 15th November 2021 a inda za’a rufe a ranar Litinin 22nd May 2022. Dukkan daliban da keda sha’awar shiga wannan makaranta sai su ziyarci application portal na makarantar a rcapplications.nda.edu.ng a inda zasu zabi “purchase form” a inda zasu biya N3,500 ta remita, kadai kudin da aka biya ta wannan hanya ne za’a amince dashi.

Dukkan sharudodi da ka’idoji na sanye a shafin wannan shafi rcapplications.nda.edu.ng domin karantawa da tabbatarwa an cika dukkan sharuda. Sannan dukkan dalibin da keda sha’awar shiga NDA wajibine yazamo ya sanyata a first choice a JAMB PORTAL. Hakana kuma dukkan undergraduates programme dama sauran bayanai na sanye a wannan website na makarantar.

Website: www.nda.edu.ng

Application portal: rcapplications.nda.edu.ng

Email: afsbdirectorate@yahoo.com

Domin Karin bayani sai a danna wannan link: https://www.ndaapplications.net/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button