Education

ABU ZARIA TA FITAR DA LOKACIN FARA POST UTME/DE REGISTRATION SCREENING- 2021/2022

Hukumar jami’ar Ahmadu Bello University Zaria ta sanar da ranar fara registration na Post UTME Screening Exercise na shekarar 2021/2021.

Hukumar jami’ar makarantar tace duk dalibin daya zabi makarantar a First Choice a kuma ya cika dukkan ka’idojin makaranatar kamar Cut-off mark 180 daya garzaya shafin makarantar domin yin wannan registration wanda za’a fara daga 13th September zuwa 3rd October 2021.

Hukumar makarantar tace daliban da suka nemi makarantar ta DE (Direct Entry) zasu biya screening fee sannan zasu dora dukkan takardunsu. Domin yin wannan registration sai a ziyarci portal na makarantar https://portal.abu.edu.ng/forms ko kuma a danna 2021/2022 post UTME Registration a website na makaranatar.

Za’a biya N2000 kudin registration exercise fee ga kowane dalibi. Za’a biya kudin a ta Remita ko POS  da makarantar ta tanadar a Campus. Domin Karin bayani sai danna wanna link domin karanta Special Bulletin na Makarantar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button