Education

ƘUNSHI A HANNU NA IYA HANA ƊALIBAI MATA UTME REGISTRATION 2022

Gamayyar rukunin masu café na Arewacin Nigeria wato “Northern cafes” na kara kira ga ɗaukacin ɗalibai mata waɗanda zasu zana jarrabawar UTME  su fahimci cewa ba hanasu ƙunshi akayi anaso su su guji yin ƙunshin ne a bikin sallar bana idan sun san suna daga cikin masu zana jarrabawar.

Wannan sanarwa ta fito ne daga kwararrun masu haɗa rijistar DE/UTME da sauran registration cewar ana mutukar fuskantar tarnaki da ƙaƙanikayi idan ɗaliba mace tanada  ƙunshi a yayin  da tazo yin dangwalen yatasa wato “Tumb Print” na registration na jarrabawar UTME (Unified Terciary Matriculation and Examination)

Wannan sanarwa ta bayo ne a samakon cewar a wannan shekara jarrabawar JAMB/UTME tazo ne a lokacin bikin sallah wanda mafi yawan dalibai mata na cikin sha’anin bikin Sallah wanda hakan kansa kaga kowace mace na dauke da adon kunshi a hannu da kafa. Bisa haka ake bawa dukkan daliban da zasuyi wannan jarrabawa da kada ta yi ƙunshi domin kaucewa fuskantar matsalar Tumbprint.

Kwrarrun na ƙara kira ga ɗaukacin ɗalibai mata dasu sanya ado wanda bazai basu matsala ba, domin gwangwajewa wajan bikin sallah ta wannnan shekara. Sanya kunshi a kan babban yatsa na hana na’urarr da ake tumbprint ganin yatsan da akayi ƙunshin don haka idan za’ayi ƙunshi a tabbatar anyi shi ne a saman hannu ba a kan ɗan yatsan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button