Education

Abubakar Tabawa Balewa University, Bauchi Online Screening 2020/2021

Hukumar makarantar ATBU (Abubakar Tabawa Balewa University) Bauchi ta fitar da sanarwar fara Online Screening ga wadanda suka zabi makarantar a matsayin First Choice a shekarar 2020/2021 sannan kuma suke da maki 180 a jamb dinsu. Suma wadanda suka nemi makarantar ta hanyar DE (Direct Entry) zasuyi wannan tantancewa a shafinsu portal.atbu.edu.ng a inda kowa zaiyi uploading data dinshi kamar haka:

  1. Dalibi zai cire RRR (Remita Retrieval Reference) da Jamb Number a matsayin User Name sai kalmar password a password (default Password)
  2. Dalibi zai biya N2000 a matsayin ga ATBU account a kowane banki a online fee
  3. Dalibi zai cike dukkan bayanan daya danganceshi ya kuma sanya hotansa
  4. Dalibi zai cire screening acknowledgment slip domin yin physical screening
  5. Za’a bude portal din har tsahon sati daya a inda zai fara daga ranar Saturday 16th zuwa Friday 22nd January 2021.
  6. Dalibi zai tahoda original credentials wajan tantancewa (physical screening) a faculty.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button