Education

Ahmadu Bello University, Zaria ta Sanar da Ranar Bude Makaranta

Ahmad Bello University ta sanya ranar 25th January, 2021 ranar bude makaranta dan cigaba da karatu, hakan yafaru ne sakamakon sanarwar da gwamnatin tarayya tabayar da kuma gwamnatin jihar ta Kaduna.

Wannan bude makaranta yasami sahalewa ne sakamakon meeting da masu ruwa da tsaki na makarantar suka gudanar (Senate of the University) a zamansu na 501 wanada akayishi a ranar 12th January, 2021 a inda masu ruwa da tsakin sunka rattaba hannun kammala karatun 2019 zuwa 2020.

Hukumar makarantar takara da cewa bude makarantar na daga cikin janyewar yajin aikin da hukumar ASUU tayi tare da bada umarnini NUC (National University Commission) hade da shawarwari na Presidential Task Force na COVID 19 na abude makarantu a ranar 18th January,2021 a karkashin Ka’ida da sharuda na COVID 19 (COVID 19 Protocols ).

Za’a bude makarantar ne a hankali a hankali bisa matakai kamar haka:

First Phase

  1. All graduating/final year Students
  2. 100 and 200 levels students
  3. All clinical medical students
  4. All post graduate students to be handled virtually using online ICT supported blended teaching and learning arrangement.

Second Phase

  1. All other non-graduating classes
  2. 300 level in the case of 4-year degree Programme     
  3. 300 and 400 levels in the case of 5-year degree Programme  
  4. 300, 400 and 500 levels in the case of 6-year degree Programme

Hukumar Makarantar na kara jan hanakalin dukkan Dalibai da subi dukkan sharuda da ka’idoji na COVID 19 a ciki da wajen Makaranta. Hakana kuma ya zama wajibi ga dukkan Dalibai dasu ziyarci shafin makarantar domin cike form na sharudan COVID-19  domin rashin cikewa da kuma turawa izuwa shafin da makarantar samar to Dalibi ba zai sami damar cire katinsa na Jarrabawa ba (Exam Card).

Hukumar makarantar ta kara tabbatar da kokarinta na samar da dukkanin kayan aikin da yakamata na kariya domin magance wata matsala da ka’iya faruwa. Daga karshe Hukumar ta kara jaddada kudurinta na samar da cikakken tsaro ga makarantar da kuma Dalibai baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button