Opportunities

An Canjawa Wasu Daga Cikin Waƌanda Suke Cin Moriyar Shirin N-Power Wajen Aiki

Wasu daga cikin beneficiaries na shirin N-Power sun fara samun  canji na wuraren da suke suke aiki kamar yadda hakan ke faruwa a halin yanzu, dayawa daga cikin masu cin moriyar basu san an samu wannan canji ba kamar yadda wani  mai cin moriyar yafadawa arewatalent.

Idan kana daga cikin wadanda suke cin moriyar sai ka hanzarta ka duba dash board dinka na N-Power sannan idan ka sami canjin sai kayi print na sabuwar PPA Letter wace zaka kai sabon wajen da aka canja maka domin suyi sign.

Bayan an kammala sign abinda zakayi na gaba shine sai adawo da takardar ta PPA café  domin ayi scanning sai ayi uploading.

Daga nan shikenan idan da wani Karin bayani hukumar zata sanar  ta email din da akayi rijista dashi.

Wannan dai shine tsarin shirin N-Power wanda akeyiwa lakabi da Batch C wanda sune ke kwasar dabgen damokaradiyya na wannan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button