Education

An Saki Sakamakon Jarrabawar NBAIS 2021/2019

Sakamakon jarrabawar ta NBAIS ya jima bai fitoba sakamakon wasu gyare gyare da hukumar shirya jarrabawar keyi a shafin su na yanar gizo-gizo (portal) wannan dalili ne yasa aka duki tsawon lokaci ba saki sakamakon ba.

Hukumar ta NBAIS tayi hakan ne domin ƙara inganta shafin da kuma ƙara masa wasu canje canje da zasu daɗawa shafin armashi.

Ɗalibai dai da suka zauna wannan jarrabawa da dama sun sha dab-dala a wajen masu café domin duba sakamakon jarrabawar duba da yadda ɗalibi ke son ganin wane irin sakamako yasamu domin sanin inda ya dosa a karatun nasa, saidai hakan bai samu ba a wancan lokaci, amma yanzu komai ya daidaita.

Muna fatan wannan gyara yazama ya tsaya sosai ba tare da samu wata tangarɗa ba a nan gaba, sannan muna kira ga dukkan Ɗalibai da suka duba nasu sakamakon idan yayi kyau da su ƙara dagewa izuwa mataki nagaba.

Sukuma waɗanda basu sami sakamako mai kyau ba kada su sare muna kiransu da suƙara zage dantse domin nasara a haka take zuwa, a faɗi a atashi watarana za’a dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button