Education

An Saki Sakamakon Jarrabawar Science and Technical Schools Board Kano

Hukumar shirya jarrabawar Science and Technical Schools Board ta sanar da sakin jarrabawar Senior Secondary (SS) da kuma ta Junior Secondary Schools domin daliban da suka zauna wadannan jarrabawar dasu duba don sanin sakamakon jarrabawar tasu.

Za’a duba jarrabawar ne da shafin makarantar a inda dalibi zaiyi amfani da hanyar da akabi wajan yin rijista domin duba sakamakon.

Hukumar makarantar ta sanar da wannan sanarwa ne a shafinta na facebook da kuma website na makarantar.

Dalibai ko Wakilansu zasu iya duba wannan sakamako ta wayar hannunsu, hanyoyin duba sakamakon jarrabawar sune kamar haka:

  1. Za’a shiga shafin makarantar na yanar gizo gizo https://www.stsbkano.ng/
  2. Sai a danna alamar aka rubuta Login mai blue din rubutu
  3. Sai a saka Username da kuma Password na dalibi wanda yana jikin takardar da akayi rijista tun a baya.
  4. Da an saya wannan bayanai sai a danna alamar dake kasa Login
  5. Daga nan sai sakamakon zai bude sai ayi printing

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button