News

ATM Card Zai Daina Aiki a Sabuwar Shekarar 2023

Babban Bankin Kasa wato CBN tare da NIBSS, Banks sun kuduri sabinta dukkan katin ATM (Debit Cards) na dukkan ‘yan kasar nan a sabuwar shekarar da zamu shiga.

Cikin wannan wata ne alummar Najeriya suka tsinci kansu cikin yanayin juyayin da jimamin Sabunta Kudi daza’a yi, kafin a kammala sai kuma ga wannan tsari shima ya biyo baya na sabunta ATM Cards.

Cewar Darakta Owoh CBN ta riga ta sahale da yin wannan lamari na sabunta ATM card, ya kuma kara da cewa sabon katin na ATM zai zama mai tsaro gami da sauki wajen charge.

Bugu da kari shi wannan sabon kati zai zama yana aiki ne a iya Nigeria tare da kasuwannin da muke dasu na nan gida kamar yadda aka lasafta a kasa:

  • Micropayment and credit
  • e-government
  • Identity management,
  • Transportation
  • Health and agriculture

Yin amfani da wannan hanya zai kawo karshen yawan amfani da takardun kudi inda hakan zai karfafa tsarin nan da CBN ta tanadar na (Cashless Policy)

NIBSS ta fitar da rahoto dake nuni da cewa cikin wata 9 ‘yan damfara sun nemi su damfari alumma har sau 46,126 wanda kuma sunyi nasara a 41,979.

Wannan ya nuna cewa kaso 91% cikin 100 ne suka fada cikin damfarar inda adadin kudin da aka damfara yakai 5.2 billion Naira cikin wata tara.

Muna fata wannan canji yazama alkhairi ga dukkan yan kasa.

Source: Legit.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button