Recruitment

BREAKING NEWS: N-POWER BATCH-C ZASU FARA KARBAR KUDADENSU

Hukumar NASIMS dake shirya  N-power ta kara dora updates na payroll a dashboard na kowane wanda ya nemi N-power Batch C na shekarar 2021

Hukumar ta sanar da cewar duk wanda baiga an sanya masa alamar biyan kudin  wato Payroll a dashboard dinsa ba to kada ya damu hukumar na iyaka kokarinta na sanya payroll ga duk wanda ya nema a dashboard dinsa.

Hukumar ta kara da cewar duk wadanda suka sanya account numbers na wadannan bankuna ne zasu riga karbar kudedensu kamar haka:

  1. United Bank for Africa (UBA)
  2. First Bank of Nigeria
  3. Guarantee Trust Bank (Gt bank)

Don haka hukumar na kara kira ga duk wadanda suka nema koda ba wadancan bankunan suka saka a dashboard dinsu ba  cewar zasu sami kudadensu dazarar an kammala dukkan gyare gyare.

Menene N-power Payroll?

N-power payroll shine jerin mutane wadanda hukumar N-power ta fitar wadanda zata biya kudadensu na N-power kamar yadda hukumar ta tsara a karkashin biyan kudade na wata wata.

Duk wanda ya kammala cekewa da dora dukkan abubuwan da aka bukata zai iya ganin pajinsa ya nuna Payroll daga gebe wanda hakan ke nuna hukumar tagama tantanceshi a inda zai jira fara karbar kudinsa nan bada dadewa ba

Wadanda shafinsu ke nuna pending kuma, hakan na nuna cewar watakil sunada “yar matsala a physical verification dinsu da sukayi amma baya nuna bazasu shiga cikin wadanda zasu amfana ba.  Hukumar ta bayyana cewar tananan tana aiki wajan ganin ta gyara dukkan wata matsala da mutane ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button