Education

Daƌumi Ɗumi: Nan Babu Ɗaƌewa Ɗaliban Jami’o’i Zasu Koma Aji, FG

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, nan babu dadewa daliban Najeriya zasu koma ajujuwansu domin cigaba da karatu.

Kamar yadda Sanata Ngige, ministan kwadago da aikin yi ya bayyana yayin taron FEC, a halin yanzu ana hango karshen yajin aiki.

a musanta zargin da ake ta yadawa kan cewa gwamnatin tarayya na kokarin kawo wani sabon salon biyan ma’aikatan albashinsu.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ana dab da komawa karatu nan babu dadewa saboda yadda ta mayar da hankali wurin shawo kan matsalolin kungiyoyin jami’o’i.

Kungiyar malaman jami’o’i msau koyawa, ASUU, Kungiyar ma’aikatan jami’o’in da basu koyarwa, NASU da Kungiyar Manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU duk suna yajin aiki.

A yayin jawab a taron majalisar zartarwa ta tarayya, FEC wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa dake Abuja, ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya ce ana hangon karshen yajin aikin.

Ministan wanda ya musanta zargin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya na shirin samar da wani sabon salo na biyan kungiyoyin, yace gwamnatin ta yi kira ga cibiyoyin, har da NITDA domin ta yi bayani kan nasarar da aka samu kan abinda ya kawo yajin aikin.

Ngige yayin jawabi, yace gwamnatin tarayya tana da burin ganin dalibai sun koma makaranta, Daily Trust ta ruwaito.

Yace taron ranar Alhamis ana tsammanin zai duba rahoton cigaba wanda cibiyoyin da ke kula da rikicin da suka hada da NITDA kan yadda ake ciki a bangaren gwajin ingancin UTAS wanda ASUU ke son a yi mata amfani da shi tare da U3PS wanda SSANU da NASU k.

(Legit Hausa)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button