Education

Da Ɗumi-Ɗumi: An Saki Sakamakon Jarabawar JAMB 2022 a Najeriya

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka zana.   

Shugaban sashen hulda da jama’a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton TheNation.

Ya bayyanawa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho

A cewarsa, su tura sakon akwatin SMS ‘UTMERESULT zuwa 55019 a wayar da aka musu amfani wajen rijista.

“Don duba sakamakon UTME, abinda kowani dalibi ke bukatan yi shine tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da akayi amfani wajen rijista, za’a turo musu sakamakon.

“Wannan shine hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai.”

Sannan kuma dalibi zai iya amfani da official shafin yanar gizo-gizo na hukumar wanda ta samar domin duba sakamakon jarrabawar.

Idan za’ayi amfani da hanyar dubawa skamakon na farko wato ta hanyar USSD Code wajibine dalibi yayi amfani da layinsa da yayi rijista ta jamb sannan kuma ya kasance akwai kudi a layin wanda ban a bonus ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button