Technology

Facebook, WhatsApp, Instagram sun katse A kasashe da Dama

Facebook da WhatsApp da Instagram sun katse, abin da ya shafi miliyoyin masu amfani da shafukan a duniya.

Kafofin sun daina aiki a Washington na Amurka da Paris da London da sauran biranen duniya.

Matsalar ta shafi masu amfani da shafukan a Najeriya.

Daya daga cikin shugabannin Facebook ya faɗa a Twitter cewa suna ƙoƙarin gano matsalar da daidaitawa cikin gaggawa.

wannan matsala da tafaru ne a yau 4 ga watan Oktoba 2021 inda mutane suna nan sunyi dako domin suga komai ya daidaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button