Education

FEDERAL GOVERNMENT ACADEMY SULEJA SCHOLARSHIP INTO JSS1 2021

Federal Ministry of Education, Federal Government Academy Suleja, makaranta ce dake samarda kwararrun yara (gifted and talented children) daga matakin secondary na JSS1 a inda gwamnatin tarayya ke daukar dukkan dawainiyar karatunsu kama daga Tuition fee, boading, feeding, uniforms, mattresses da kuma basic text book/exercise.

Wannan program na mutukar la’akari ne da daliban JSS1 wadanda suke da mutukar fasaha da fahimta (the Gifted Education Program) domin kammala karatunsu don samarda zakwakuran daliban dake a fadin kasarnan.

KARANTA: AL-ISTIQAMA UNIVERSITY KANO SCHOLARSHIP 2021

Za’a fara dauka a ranar Asabar 3rd July, 2021 a duka Geopolitical Zone guda 6 dake fadin kasarnan. Za’a iya cike daya daga wadannan santoci kamar haka:

  • FGA, Suleja
  • FGC, Sokoto
  • FGGC, Onitsha
  • FGC, Warri
  • FGGC, Bwari
  • FGGC, Benin
  • FGGC, Umuahia
  • FGGC, Kabba
  • FGBC, Apo
  • FSTC, Yaba
  • FGC, Portharcourt
  • FGC, Billiri
  • FGC, Keffi
  • FGGC, Oyo
  • FGC, Calabar
  • FSTC, Ilesa
  • FGC, Ilorin
  • FGGC, Gusau
  • FGGC, Gwandu
  • FGGC, Shagamu
  • FGC, Jos
  • FGC, Maiduguri
  • FGGC, Abaji
  • FGGC, Potiskum
  • FGGC, Bida
  • FGGC, Bauchi
  • FGC, Minna
  • FGC, Enugu
  • FGGC, Akure
  • FGGC, Yola
  • FGGC, Imiringi
  • FGGC, Kaduna
  • FGC, Wukari
  • FGC, Ikole Ekiti
  • FGGC, Zaria
  • FSTC, Otukpo
  • FGC, Kiyawa
  • FGC, Kano
  • FGGC, Gboko
  • FGGC, Ezzannagbo
  • FGC, Daura
  • FSTC, Uyo
  • FGGC, Owerri

WADANDA SUKA CANCANTA:

  • Wajibine dalibi yazama yanada shekara 11 a dai dai da December 2021
  • Dolene dalibi yazamo ya kammala Primary Six a dai dai da 2021 academic year
  • Dolene dalibi yazo da wani documents wanda zai gamsar da bayanin sama na farko ko na biyu

YADDA ZA’A CIKE:

Za’a ziyarci wannan website: www.fedacademy.org ko www.education.gov.ng a inda za’ayi downloading na form a cike sannan ayi submitting kodai online ko kuma ta courier service.

LOKACIN RUFEWA:

Juma’a 25th June, 2021.

Hukumar tace babu wani Application form da za’a saurara bayan rufewa don haka ayi kokarin cikewa akan lokaci.

KARANTA: Dalilan Da Yasa Hukumar NECO ta Daga Jarrabawar National Common Entrance Examination (NCEE) 2021

Note: za’a sanar da duk daliban da sukayi nasara a website Federal Ministry of Education da kuma website na wannan makaranta. Dalibi zaije daya daga cikin wadancan santoci da pen, pencil, Eraser, Ruler, crayon da kuma passport photographs.

Domin samun cikakken bayani gameda wannan program: 08034130004, 08065027279, 08035802249, 08096270975

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button