Recruitment

FEDERAL GOVERNMENT TA SAKI LIST NA N-POWER BATCH C

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da sanar da sakin list na N-POWER Batch C a inda sanarwa ta fito ne ta shafin yanar gizo gizo (website) na hukumar NASIMS (National Social Investment Management system).

Gwamnatin tace dukkan wanda ya nemi wannan program daya tabbata ya sabunta bayanansa sannan ya tabbatar yayi gajeriyar jarrabawar da hukumar ta fito da ita domin ganin mutum sami damar shiga jerin mutanen da zasu bayyana a jerin list da hukumar ke fitarwa.

Hukumar ta kara da cewa zata turawa kowane wanda ya nemi wannan program email wanda ke bayyana mataki na gaba. Sauran wadanda basu sami email ba zasu jira zuwa wani Batch domin sake neman wannan shiri da zarar an sake budewa.

Idan za’a iya tunawa gwamnatin ta tabbatar da cewar duk wadanda sukayi nasarar wannan program za’a daukesu ne a karkashin shirin nan na daukar aiki na N-power. Sadiya farouk (minister of humanitarian management and Social Development) ce ta sanar da hakan inda takara da cerwar gwamnatin ta dauki ingantaccen mataki wajan yin wannan regista, tantancewa da kuma dora wadanda sukaci akan tsarin biya na N-power wanda dukkan wadannan zasu kasance ne Online a matattara daya.

Daga karshe minitan takara da cewar sun bude wannan hukuma ta NASIMS ne domin tabbatar da ganin komi na tafiya dai wadaida kamar yadda gwamnati tayi alkawari.

Domin karin bayani: https://nasims.gov.ng/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button