Education

Gwamnatin Jihar Kano ta Biya Kimanin Million N50 Domin Sakin Jarrabawar NECO

A ranar Laraba 13TH January, 2021 hukumar jarrabawar NECO ta saki sakamakon Jarrabawar Neco a duka fadin kasa.

Sai dai wasu jahohin daga cikin jahohi 36 na kasa hukumar NECO ba ta saki nasu sakamakon makarantun gwamnati ba, saboda wasu kudade da gwamnatin ba ta biya ga hukumar NECO ba.

Amma duka makarantu masu zaman kansu tuni nasu sakamakon yafita tun ranar da hukumar NECO ta saki.

Hakana anan Jihar Kano gwamnatin jihar ta biya hukumar NECO million hamsin kamar yadda kwamishinan ilimi na jihar ya bayyana Muhammad Sanusi Kiru a ranar Juma’a yayin da ya zanta da manema Labarai a fadar gwamnatin kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button