Education

GWAMNATIN KANO TA KARA HUTUN MAKARANTU

Gwamnatin jihar Kano ta bakin Kwamishinan Ilimi na jihar Dr. Sanusi Muhammad Kiru ta sanar cewar ta kara sati daya ga “yan makarantun kwana da na jeka ka dawo.

Gwamnatin ta kara lokacinne duba da watan Azumi da za’a shiga wanda hakan zai bawa iyaye da yaran damar kara kintsawa da kuma fara Azumi kafin ranar da za’a koma.

Makarantun kwana zasu koma a ranar 18 ga wannan watan (18th April, 2021) sai makarantun jeka ka dawo kuma zasu koma a ranar 19 ga wannan wata (19th April 2021).

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button