How to Apply Into Emirates College of Health Sciences and Technology for 2021/2022
Yadda za’a cike makarantar koyon kiwan lafiya ta Emirates College Of Health Sciences and Technology
Domin cike wannan makaranta sai a bi wadanan matakai kamar haka:
Bayan an shigo website na makarantar https://ecohsat.admissions.cloud/
Mataki na farko shine Account Activation:
1. Za’a danna New Application
2. A shigar da Suma, valid phone number (ka tabbatar lambar wayar tana aiki)
3. Fejin zai kaika inda zaka shiga wato LOGIN
mataki na Biyu:
Zakayi amfani da lambar wayarka da shigar a farko wadda itace zata zama Username da Password naka. Sai ka danna kashiga cikin fejin
Mataki na uku:
Zakaje gurin biyan kudi. Ka tabbatar ka sanya sunanka dai dai sannan ka biya kudin, bayan biyan kudin sai ka cike dukkanin bayananka.
Mataki na hudu:
Za’a zabi programme da ake son yi daga jerin courses da makarantar ke gabatarwa.
Mataki na biyar:
Za’a sanya educational qualification wato takardun makaranta kamar WAEC/NECO da dai sauransu. Ba’a bukatar sama da zama biyu na jarrabawa. A tabbatar an sanya kara kara inda aka zauna jarrabawa sannan a sanya exam number ta fito sosai.
Mataki na shida:
Za’a dora photo. A tabbatar an sanya photo wanda zaa iya gane mutum sannan yazamo yanada fari ko wata kala wadda zaa iya gane mutum. Hoton yaza a JPEG yake sannan kada nauyinsa ya wuce 150kb.
Mataki na bakwai:
Bayan antabbatar an cike bayanai dai dai, sai a tura wannan apllication.
Mataki na takwai:
Za’ayi printing na Application form. Zaaga lambar waya wadda aka cike ita zata Application ID sannan kuma itace Login details. Sai ayi printing na Application form.
Mataki na tara:
Kafin a Nada admission sai an tabbatar da wadannan abubuwa kamar:
I. Wajibi a halarci screening, ba wakilci ba
2
II. Wajibi azo gurin screening da dukkan takardun makaranta da wadanda aka cire a yayin application
Iii. Za’a bada photocopy na wadannan takardu
iv. Za’a bada photocopy na indigene letter da takardar haihuwa
Matakai na goma:
Makarantar zatayi amfani da lambar wayarka wajan tuntuba gameda lokacin da zaa gudanarda wannan screening.
Domin karin bayani gameda wannan makaranta sai a tuntubi wadannan lambobin waya na makarantar 08063424228, srmssupport@flexisaf.com, saadanas@flexisaf.com