Networking

Yadda Ake Hada NIN da Layin MTN, Airtel, 9mobile, Glo ta Hanya Mai Sauki

Kamar yadda yazama wajibi dukkan wani layin waya sai an hada shi tare da National ID Card sannan zai cigaba da aiki kamar yadda ya kamata, Rashin hada layin da NIN ka’iya jawowa a kulle layin gaba daya.

Bayan haka kuma kowane kamfani daga cikin kamfanin sadarwa MTN, Airtel, Glo da 9mobile sun bayar da hanyoyin hade layin da NIN, hanyoyin sune kamar haka:

Yadda Ake Hada NIN da Layin MTN

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *785# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko kuma ayi amfani da mobile app na MTN mai suna myMTN app, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN Number din ta shafin yanar gizo gizo da MTN suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link https://nin.mtnonline.com/.

Yadda Ake Hada NIN da Layin Airtal

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *121*1# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko kuma ayi amfani da mobile app na Airtel mai suna My Airtel, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafin yanar gizo gizo da kamfanin Airtel suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link https://airtel.com.ng/nin/

Yadda Ake Hada NIN da Layin 9mobile

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *346# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko kuma ayi amfani da mobile app na 9mobile mai suna My9mobile, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafin yanar gizo gizo da kamfanin 9mobile suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link https://9mobile.com.ng/nin/

Yadda Ake Hada NIN da Layin Glo

Za’a iya amfani da wadannan lambobi *346# inka sanya su saika danna kira zai baka dama kasanya lambobin NIN wato National ID Card guda goma sha daya (11) ko kuma ayi amfani da mobile app na Glo mai suna Glo Café Nigeria, shima ta cikinsa zai baka dama kahade layinka da NIN Number.

Sannan kuma za’a iya shigar da bayanan NIN din ta shafin yanar gizo gizo da kamfanin Glo suka bayar domin wannan aiki kawai, Danna wannan link http://mobileapp.gloworld.com/glonin/home

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button