Education

Hukumar Jamb Ta Soke UTME Cut Off Marks Na 2021

Hukumar Jamb ta soke UTME Cutt Off Marks a wajen samun admission ga sabbin dalibai wadanda zasu shiga jami’a, Hakan yabiyu bayane inda hukumar ta jamb ta bawa jami’o’in kasar nan ‘yanci dasu zabi maki mafi can-canta da zai bawa kowane dalibi damar shiga jami’a.

Wannan tsari an tattauna shi ne a meeting din da hukumar ke yi (2021 Policy Meeting), wanda ministan ilimi na kasa Mal. Adamu Adamu ya jagoranta.

A lokacin da ake gudanar da wannan meeting rijistara na Jamb Prof. Ishaq Oloyede, yace wasu jami’o’in kasar nan kamar irin su University of Mai Duguri sun zabi makin yakasance 150, Usman Dan Fodiyo University da Sokoto sun zabi 140, hakana Pan Atlantic University sun zabi 210, Lagos State University 200, Covenant University 190, Bayero University, dake Kano ta sanya 180.

Oloyede yakara da cewa gameda admission wajibine dalibai suyi uploading na credentials dinsu a central admissions processing system (CAPS) wanda hakan zai sa daliban su sami damar samin admission ta inda dalibi zaiyi accepting na admission offer a karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button