Education

JAMB/UTME SLIP REPRINT COMMENCES 2022

An fara cire Slip na JAMB (Jount Admission and Matriculation Board) na wannan shekarar a inda dalibi zai rana, Lokaci da wurin da zai zauna wannan jarrabawa kamar haka.

A yau ne hukumar ta bada damar fara cire wannan slip domin dukkan daliban da sukayi rejistar su iya ganin rana, lokaci da wurin da zasu zauna wannan jarrabawa a duka fadin kasarnan.

Wannan bayanai ya nuna cewa abun yazo inji mai tsoron wanka! Dan haka dukkan dalibai sai su kara zage dantse kuma su kara kaimi domin tunkarar jarabbawar ta bana domin kuwa hukumar ta tsayar da ranada lokaci domin komai ya tafi kamar yadda ta tsara.

Sannan a wani bangaren daban kuma an gargadi dalibai mata da su guji amfani da kunshi mai a lokacin jarrabawar domin kuwa yatsu basu cika daukar na’urar thumb print ba kuma duk wace batayishi ba ba zata zauna jarrabawar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button