Education

Jami’ar Lagos Zata Fara Post UTME Screening Exercise Na Shekarar 2020/2021

Jami’ar jahar Lagos zata fara aiwatar da jadawalinta na POST UTME na shekar 2020/2021.

Wannan jami’a ta shirya tsaf domin daukar sabbin dalibai dake fadin kasarnan bakidaya musamman wadanda makinsu na jamb yakai 200 zuwa sama.

Also read: CBN Ta Gargadi Yan Nigeria Kan Sabbin Yan Damfara Ta Yanar Gizo-Gizo

Abubuwan da kowane dalibi ke bukata kafin zuwa wannan tantancewa sune kamar haka:

  1. Ya kasance jami’ar Lagos ce zabinsa na farko (first choice)
  2. Makin dalibin na jamb yazama yakai 200 zuwa sama
  3. Dole kowane dalibi yazama yanada jarrabawar sakandare kuma yayita ne a zama daya (one sitting), sannan ya zama yanada 5 credits wanda ya hadar da Maths da English.
  4. Dole ne dalibi yazamo yakai Shekara Goma Sha Shida (16 years old), a 31 October, 2020, idan ba hakaba to kada ya nemi wannan jami’a.

Also read: Kust Wudil Post UTME/Direct Entry Screening 2020/2021

Sannan wannan jami’a ta kara da cewa dukkan dalibin da bai halacci wannan tantancewa ta POST UTME ba to kada ya sa raid a samun gurbin karatu a wannan jami’a.

Sannan jami’ar ta kara da cewa dukkan dalibin da aka koreshi a sakamakon rashin dagewa kokuma fashi zai iya sake neman wannan jami’a amma bisa sharadin na ba lallai bane a bashi abinda ya nema sai abshi wani abinda ya dace dashi. Hakana duk dalibin da aka tasa keyarsa aka fatattakeshi to baza’a bashi damar sake neman wannan jami’a ba.

Akarshe  Arewa Talent na shawartar matasan kasarnan dake da sha’awar karatu da su nemi wannan jami’a da kada suyi la’akari da nisanta ko kuma wani abu daban saboda shi ilimi shine hasken rayuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button