Education

KALLI JERIN JAHOHIN DA SUKAFI SATAR AMSAR JARRABAWAR NECO

Shugaban Hukumar Neco Dantani Wushishi ya sanar da jahohin da suka fi kowanne yawan magudin jarrabawa a yayin bayyana mukala mai taken “Consequences of Examination Malfarctice: closing the gaps and incentives for National Growth” a taron 2021 Biennial National Conference and AGM of the Association of model Islamic Schools.

A yayin wannan bita shugaban hukumar Neco ya bayyana cewar jahohin da sukayi fice wajan magudin sune kamar haka:

A shekarar 2020 wadannan jahohi ne a gaba gaba kamar haka:

  1. Adamawa ce kangaba wajan magudin jarrabawa da kimanin adadin 18.51%
  2. Bauchi na daga 7.88%
  3. Kaduna kuma nada 6.87%
  4. Kano nada 7.88% katsina nada 18.01%

Shugaban yace a tsahon shekaru biyar da suka shige jahohin Bauch, Borno, Kano da Kebbi ne suka fi kowace kawadanne jahohi tabka magudin jarrabawa. Shugaban yace fitar takardar jarrabawa, taimakekeniya da kwafi kwafi na kan gaba wajan bada tasgado ga ingancin sakamakon jarrabawa inda hakan ke samar da tasgado wajan sahihancin ilimi.

Shugaban ya roki gwamnati data maida hankali kan wadannan matsal tsalu ta kuma samar da hukunci mai zafi kan duk wanda aka samu da magudin jarrabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button