Education

KANO UNIVERSITY OF SCIENCE AND TECHNOLOGY WUDIL ZATA FARA POST UTME DA DE ADMISSION SCREENING 2021/2022

Hukumar makarantar Kano University of Science and Technology, Wudil ta sanar da fara registration na Post UTME da Direct Entry (DE) Admission Screening Exercise ga daliban da suka nemi wannan Jami’a a first choice na shakrar 2021/2022.

A. WADANDA ZASU IYA YIN WANNAN REGISTRATION:

  1. Duk dalibin da yake da maki 120 na UTME.
  2. Direct Entry Applicant wanda yake da akalla Lower Credits a National Diploma ko akalla 7 points a NCE ko IJMB a course da keda alaka da abinda ya nema ne kadai zasu iya biyan kudin a online payment na makarantar.

B. YADDA ZA’AYI REGISTRATION:

  1. Za’a ziyarci wannan website na makarantar www.kustwudil.edu.ng sai a danna 2021 post UTME/Direct Entry Screening Registration.
  2. Create account ta hanyar amfani da IAMB UTME/Direct registration number sannan a kirkiri password wanda akeda bukata.
  3. Za’a biya N2,000 (Non refundable) ta hanyar amfani da master card ko Visa Card ko biya kai tsaye a banki.
  4. Bayan an biya said alibi ya cigaba da registration a inda zai zuba o’level results sannan masu DE kuma zasuyi scanning na IJMB ko NCE result/certificate dinsu.
  5. Sai a danna submit sannan ayi printing na UTME/DE Acknowledgment slip

C. LOKACIN YIN REGISTRATION:


Za’a fara wannan registration a ranar Litinin 18th October zuwa 12th November 2021

Note:


Hukumar makarantar zata sanar da Wuri, lokaci da ranar fara wannan registration ga dukkan daliban da suka nemi wannan jama’a.

A ranar wannan screening exercise kowanne dalibi zaizo da print out na Acknowledgment Slip

Dalibi daya dora O’level result (NECO, WAEC DA NEBTEB) wanda bai wuce na zama biyu ba.

Duk dalibin da sakamakon jarrabawarsa bai fita ba daya danna Awaiting Result a yayin Registration.

Duk dalibin da baiyi wannan registration a lokacin da aka bayyana ba bazai samu damar samun admission ba.

Wannan sanarwa ta fito daga bakin Alh. Aminu Bello Muhammad, FNIM Registrar na makarantar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button