Recruitment

Sabon shirin CBN na tallafawa Daliban jami’a da Polytechnic- 5 million/25 million

A cigaba da gabatar da shirye shiryen rage yawaitar dalibai masa aikinyi dake fitowa daga jami’a da polytechnic, babban bankin kasa CBN ya fito da sabon shiri mai taken Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES) wanda babban bankin zai bawa daliban da suka fito daga Universities da polytechnic a duka fadin kasa wadanda keda sha’awar dogoro da kansu ta hanyar bunkasa wata hikima ko fasaha wadda zata sa su zamo masu dogaro da kansu.

Babban bankin ya shirya bada rancen N5 million ga dalibi ko kamfanin da dalibi ya kafa ko kuma wani project da dalibin ya fara. Hakana babban bankin zai bada N25 ga kamfanin da dalibai suka kafa ko kuma wani project da dalibai suka hadu wajan gudanarwa. Akwai interest na 5℅ ga wannan bashi a inda za’a biya a tsawon shekara 5 sannan za’a fara biya bayan shakara daya da karba. Sannan daliban da suka kammala karatunsu tsawon shekara 7 zasu iya neman wannan bashi.

Ire iren sana’oin da za’a iya nemar wannan bashin dasu sune:-

  • Kasuwancin gona
  • Harkar kimiya da fasaja
  • kirkire kirkire
  • Harkar sadarwa

Abubuwan da ake bukata wajan neman wannan bashi:-

  1. Degree na farko da NYSC certificate
  2. Lambar waya wadda aka hadata da NIN, BVN, TIN da email address
  3. CAC certificate
  4. Corporate bank account

Babban bankin na mutukar maraba da mata masu sha’awar kasuwanci.

Domin shiga aci moriyar wannan garabasa sai a ziyarci wannan website na CBN domin cike dukkan abinda aka nema domin samun wannan tagomashi a https://cbnties.com.ng/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button