Education

SABUWAR HANYAR DA AKE KARBAR WAEC CERTIFICATE 2021

Hukumar shirya jarrabawar WAEC na sanar da al’umma cewar a yanzu dalibai zasu iya karbar Attestation of Result ko Certificate dinsu a kowanne office na WAEC dake fadin kasarnan.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwa ne ta bakin Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Demianus G. Ojijeogu a ranar 16th April 2021.

YADDA ZA’A KARBI ATTESTATION OF WAEC KO CERTIFICATE

A baya idan dalibi zai karbi WAEC Result ko Certificate, wajibine dalibi ya nema a jahar da ya zauna wannan jarrabawar kamar yadda yake a tsarin karbar jarrabawa na hukumar. A yanzu hukumar ta fito da sabuwar hanyar karbar wannan result ko Certificate domin sawwakawa dalibai kamar haka:

  1. Domin karbar Attestation of Result, dalibai zasu iya nema daga kowane ofishi na WAEC dake fadin kasarnan sannan subiya kudin da hukumar ta zayyana na karba.
  2. Domin karbar Certificate, dalibai zasu iya nema daga kowane ofishi na WAEC dake fadin kasarnan sannan subiya kudin da hukumar ta zayyana na karba.
  3. Wajibine dalibi ya bayyana karara ofishin da zai karbi Result/Certificate sannan kuma wajibine a biya kudin kawowa(courier service) ga inda za’a kawowa mutum
  4. Wajibine dalibi ya bayyana lambar wayarsa da email dinsa a yayin wannan nema.
    Domin Karin bayani danna wannan link: Waec Twitter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button