Education

SHIN KASAN CEWA JAMB TA DAKATAR DA AIKI DA USSD DOMIN DUBA RESULT?

Hukumar shirya jarrabawar JAMB (Joint Admission and Matriculation Board) ta sanar da tsayar da aiki da code dinta na USSD(55019) duba da yawan matsalolin da ake fuskanta. Ana amfani da wannan USSD ne wajan turawa domin a sami sakamakon jarrabawar UTME (Unified Tertiary Matriculation Examination ) wadda hukumar ta saka bada dadewaba.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin maga takardar hukumar Dr. Fabian Benjamin a ranar Asabar, 26th June 2021.

Dr. Benjamin ya kara da cewa yawaitar karafe korafe ya yawata daga dalibai wajan duba sakamakon su don haka hukamar na umartar dalibai da su ziyarci shafin humar kai tasaye domin duba sakamakonsu.

Don haka domin duba result na jarrabawar JAMB a yanzu za’ayi amfani da wadannan hanyoyi guda uku:

Jamb Result Checking portal: https://portal.jamb.gov.ng/ExamSlipPrinting/CheckUTMEResults

Enter Jamb Registration Number/Email wanda kayi rejista dashi.

Click on Result. Portal din zai turo maka da sakamakonka nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button