Education

Yadda Ake Interview Na Science and Technical Schools Board Kano

kamar yadda ya gabata bada dadewa ba hukumar Science and Technical schools board kano state ta saki sakamakon jarrabawar “yan SS da JS na wannan shekarar a inda da damar dalibai sun samu nasarar hayewa hakana da damar dalibai basu sami damar samun maki 50 ga “yan SS da kuma maki 45 ga “yan JS (Average Pass Mark) wanda hukumar ta fitar.

Wadannan maki guda 50 da 45 da hukumar ta fitar ne ke tabbatarwa dalibi ya cancanci zuwa interview da hukumar zata aiwatar a dukkan examination centers da hukumar ta fitar domin tantancewa da kuma tabbatarwa cewar wannan dalibi ya samu nasara samun kodai maki 50 na “yan SS ko 45 na “yan JS da hukumar ta fitar.

Hukumar  ta Science and Technical schools  board kano ta bayyana yadda kowane dalibi zai ziyarci examination center dinsa domin yin interview da jerin wadannan ka’idoji kamar haka:

  1. A ranar Litini 25th da ranar Talata 26th October 2021 kowanne dalibi zai ziyarci examination center da misalign karfe 8:00 na safe domin yin interview
  2. Kowanne dalibi zaizo wannan interview cikin kayansa na makaranta a cikin kamala ta dalibi
  3. Kowanne dalibi zaizo da wadannan abubuwa kamar haka:
  4. Kayan rubutu i.e Biro, pencil, sharpener, cleaner da dai sauransu
  5. Za’azo da original copy na takardar Haihuwa (Birth Certificate/Declaration of age)
  6. Examination result slip
  7. BECE Exam Card ko Original report sheet na 1st ko 2nd term na shekarar 2020/2021 na makaranatar da dalibi yake a yanzu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button