NewsOpportunities

Yadda Kalar Sababbin Kuƌin Naira suka Kasance

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da sababbin takardun kuɗin naira da ta sauya wa fasali.

An fitar da takardun kuɗin ne yayin bikin da ke gudana yanzu haka a Fadar Shugaban Najeriya ta Aso Rock Villa a Abuja.

Takardun kuɗin sun ƙunshi N1,000, da N500, da N200.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga ranar 15 ga watan Disamba zai sake su ga jama’a don fara amfani da su.

Kazalika, za a daina amfani da tsofaffin takardun a matsayin kuɗi daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.

Babban Bankin Najeriya na CBN ya ce akwai alfanu sosai game da sauya wa wasu daga cikin takardun naira fasali, waɗanda ya ƙaddamar a yau Laraba.

Cikin jawabin da Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gabatar yayin bikin, ya ce daga cikin alfanun da za a samu har da daƙile yunƙurin buga jabun kuɗi.

“Alfanun da za a samu na sauya fasalin naira na da matuƙar muhimmanci ganin cewa yunƙurin zai taimaka wajen rage hauhawar farashi ta hanyar mayar da kuɗi zuwa bankuna,” in ji shi.

“Kazalika, zai tallafa wajen gyara fasalin kuɗin da kuma samun cikakkun bayanai game da zagayawar kuɗi a tsakanin jama’a.

“Mun yi imanin cewa hakan zai jawo ƙaruwar jama’a cikin harkokin kuɗi da kuma rage amfani da garin kuɗin.

“sauya fasalin zai taimaka wajen yaƙi da rashawa saboda za a ƙara yawan manyan takardun naira waɗanda su kuma za a iya bin sawunsu daga bankuna cikin sauƙi.”

(BBC hausa)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button