Education

Yadda Za’a Sami Saƙon JAMB PROFILE CODE Na 2022 a Cikin Ƙaramin Lokaci

Yadda Za’a Sami Saƙon JAMB PROFILE CODE Na 2022 a Cikin Ƙaramin Lokaci

Related Articles

A ko wace shekara akwai dalibai masu tarin yawa da suke zana jarrabawar nan dake bada dama domin shiga zangon karatu na gaba bayan kammala Sakadare wato JAMB, saidai a duk shekara dalibai na samun ciwon kai wajen tura Saƙon JAMB PROFILE CODE da ake amfani da wayar hannu domin wani yakan tura ba adadi kuma za’a dauki kudin daga layin wansa amma bazai sami Saƙon  na JAMB PROFILE CODE ba.

Domin magance wannan matsala idan kasan ko kinsan kuna daga cikin waƌanda zasu zauna wannan jarabawa ta 2022 to yana da matukar mahimmanci a fara Text Messege na Saƙon JAMB PROFILE CODE tun a yanzu domin kowa yasani said JAMB PROFILE CODE ne za’a iya yin rijistar JAMB.

A kowace shekara yawan dalibai dake son zana Jarrabawar ta JAMB ke  jawo Network yayi nauyi, hakan yasa Arewatalent Team sukayi bincike na musamman domin sanar da al’umma yadda zasu zabtare wannan matsala dake faruwa duk shekara.

YADDA AKE TURA SMS TEXT NA SAƘON JAMB PROFILE CODE:

hukumar JAMB ta fitar dukkan jadawalin yadda dalibai zasu sayi UTME ePin tareda bayyana  yadda kowane dalibi zaibi wajan sayan wannan pin kamar haka:

1.            Wajibi ne kowane dalibi yazamo yanada NIN kamar yadda hukumar JAMB ta tabbatar

2.            Za’ayi amfani da lamabar wayar da akayi rijistar NIN wajan tura sakon profile code.

3.            Za’a rubuta NIN sai a bada space sannan a rubuta harufa 11 na NIN (11 digits number) izuwa kodai 55019 ko 66019 misali: NIN 00123456789. (A tabbatar an bada “yar tazara a tsakani kamar NIN da lambobin). Za’a daura N50 charge na wannan service.

 Note: A tabbatar sunan da aka turo ta hanyar profile code shi aka tura wajan sayan UTME ePin!

4.            Bayan anturo maka da profile code sai a garzaya izuwa CBT center mafi kusa ko kuma wadda akafi so a basu wannan profile code a inda za’ayi wannan registration.

5.            Yadda za’a dawo da profile password: za’ayi amfani da lambar da aka sayi ePin sai a rubuta “password” sai a bada space sai rubuta “email address” a tura zuwa 66015 ko 55015 ta hanyar text message

Hukumar ta JAMB ta bayyana cewar ta kara subjects guda biyu wato computer studies da Physical and Health studies. Hakan ya sanya subjects na UTME suka koma subjects 25.

YADDA ZA’A DAWO DA ePIN IDAN BAIZOBA KO KUMA IDAN YA BATA

Ga masu JAMB: Za’a rubuta UTMEPIN da lambar da akayi NIN  a tura zuwa 55019 ko 66019 a inda za’aga an turo da wannan ePin da aka rasa.

Ga masu DE: Za’a rubuta DEPIN da lambar da akayi NIN  a tura zuwa 55019 ko 66019 a inda za’aga an turo da wannan ePin da aka rasa.

Note: a tabbatar da lambar da akayi rijistar NIN aka aika wannan sako! Hukumar Jamb ta fito da sabbin USSD CODE (55019, 66019)domin saukakawa dalibai tura profile code.

Za’a fara UTME/DE Registration a ranar 12th Febuary zuwa 19th March 2022. Sai Mock registration a ranar 12th Febuary 2022 sai Mock UTME a ranar April 16th 2022. Za’a fara  Jarrabawar UTME  a ranar 6th zuwa 16th May 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button