Education

YADDA ZAKA CIKE BUK SCREENING ECERCISE 2021/2022

Kamar yadda hukumar Jami’ar Bayero University ta sanar cewar bazatayi physical screening ba wannan shekarar online screening zatayi don ga bayanai daki daki na yadda za’a cimma wannan screening kamar haka:

Na daya:

Dalibi zaije jamb portal domin yayi accepting na admission sannna yayi printing na admission letter.

Na biyu:

Za’a shiga wannan link: https://mybuk.buk.edu.ng/myScreening/ da jamb number, state of origin da gender domin duba admission

Na uku:

Sai ayi Downloading BUK admission letter, undertaking  da kuma University Health Services Registration Form ta https://mybuk.buk.edu.ng/myScreening/

Na hudu:

Sai ayi generating, download da kuma printing na BUK personalized payment form (BUKPPT) a inda za’a biya N 10,000. Bayan an biya wannan kudi ta hanyar  Remita e-payment don haka a tabbata an karanta yadda za’a biya kudin don kaucewa matsala da delay. Jami’ar ta kara da cewar bazata lamunci biyan wani kudi ba idan dalibi yayi kuskure.

Na biyar:

Sai ayi uploading na documents a jpg format  na wadannan abubuwa:

  1. Jamb slip
  2. Jamb admission letter
  3. O level result
  4. A level result  ( DE candidates only )
  5. Any other relevant documents

Za’a iya rejecting na documents idan sukayi dushi dushi. Don haka a tabbatar an dora clear picture domin idan dalibi ya fuskanci wannan matsala sai a ya jira awa 12 zuwa 24 kafin ayi approved

Na shida:

Sai ayi printing na Acknowledgment slip, wanda zai kunshi muhimman bayananka

Na bakwai:

Bayan dalibi ya dora komi dai dai sai ya cigaba inda zai fara normal registration ta wannan link: https://mybuk.buk.edu.ng/ug/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button